No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan Kano ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya rushe ɗaukacin shugabannin riƙon ƙananan hukumomin jihar Kano 44, an sanar da wannan mataki  a ranar Talatar da ta gabata, hakan ne ya kawo ƙarshen  wa’adinsu na watanni shida da suka kwashe suna jagorantar harkokin ƙananan hukumomin Jihar Kano.

Kamar yadda sanarwar ta tabbatar da umarnin da aka baiwa shugabannin riƙon ƙananan hukumomin da su mulki  ga daraktocin gudanarwar ƙananan hukumomin su .

KU KUMA KARANTA: Taron bunƙasa cinakayya tsakanin Damagaram, Daura, Jigawa da Kano

Idan za’a tuna a zaman majalisar dokokin Kano na ranar litinin data gabata saida aka gabatar da buqatar qarin watannin biyu ga shugabannin riqon ƙananan hukumomin, wanda kuma shugaban marasa  rinjaye na majalisar dokokin Jihar ya ƙalubalanci wannan ƙudirin, har sai da takai ga zazzafar mahawara data sa shugaban marasa rinjaye ficewa daga majalisan.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...