Gwamnan Kano ya naɗa sabon Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida

0
52
Gwamnan Kano ya naɗa sabon Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida

Gwamnan Kano ya naɗa sabon Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida

Daga Ali Sanni Larabawa

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya a matsayin sabon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida. Abba ya sanar da wannan naɗin ne a wurin bikin rantsar da majalisun gudanarwa na manyan makarantun jihar.

Abba ya buƙaci Manjo Idris da ya yi amfani da gogewarsa ta tsohon soja wajen inganta ɓangaren na tsaro da samar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Kimanin watanni biyar da suka gabata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙiro ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida a Kano amma bai naɗa kwamishina ba a lokacin.

KU KUMA KARANTA:Ra’ayi: Buɗaɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano

Ana sa ran naɗin tsohon babban jami’in sojan zai ƙara inganta tsaron cikin gida a Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gwamna Abba Kabir ya buƙaci Manjo Janar Idris mai ritaya da ya tunkari ayyukan da ya rataya a wuyansa da ƙwazo da fasaha irin wanda ya nuna a lokacin aikinsa na soja.

Gwamnan ya kuma nanata muhimmancin sabuwar ma’aikatar na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar ta Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here