Gwamnan Kano ya naɗa Kwankwaso, Shekarau, da Ganduje muƙamai a Jihar

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) domin ta zama mai ba da shawara ga gwamnatin jihar.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

Mambobin majalisar sun haɗa da tsaffin Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Shugabannin Majalisar Dattawa (Idan akwai), Shugabannin Majalisar Wakilai, Shugabannin Majalisar Jiha, Mataimakan Shugaban Majalisar, Alkalan Kotun Ƙoli da suka yi ritaya, alkalan Kotun ɗaukaka ƙara da suka yi ritaya, tsoffin Alkalan Kotun ɗaukaka ƙara. Manyan Alkalan Jahar, Tsofaffin Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha, waɗanda dukkansu ‘yan asalin jihar ne.

Haka kuma majalisar ta haɗa da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano, da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da naɗa su.

KU KUMA KARANTA: Mun rungumi ƙaddara a kan hukuncin Kotun ƙoli – Jam’iyyar APC a Kano

Da wannan ne Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Umar Ganduje ke zama mambobin majalisar.

Gwamnan ya jaddada ƙudirin sa na ci gaba da gudanar da gwamnati a buɗe domin tafiyar da kowa da kowa, a sabon yunƙurin na Kano na zamani.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *