Gwamnan Kano ya naɗa Akanta-Janar da shugabannin hukumomi huɗu

1
426

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Abdulƙadir Abdussalam a matsayin sabon Akanta Janar na jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar ranar Alhamis.

Ya ce Gwamnan ya kuma naɗa Garba Ahmed-Bichi a matsayin sabon Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano.

Gwamna Abba, a cewar sanarwar, ya kuma naɗa Rahila Mukhtar a matsayin Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Gudumawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano, (KCHMA).

KU KUMA KARANTA: Sabon Gwamnan Kano Abba Gida-Gida, ya naɗa shugaban ma’aikata da sakataren gwamnati

Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnan ya kuma amince da naɗin Hassan Baba-Danbaffa a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, (KARMA).

Gwamnan ya kuma naɗa Ibrahim Yakubu, Manajan Darakta na Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano, (KNUPDA).

Dawakin-Tofa ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da bikin rantsar da waɗanda aka naɗa domin samun damar karɓar ragamar mulki nan take.

1 COMMENT

Leave a Reply