Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur’ani, ya ba su kujerun aikin Hajji

0
307
Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur'ani, ya ba su kujerun aikin Hajji

Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur’ani, ya ba su kujerun aikin Hajji

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karrama gwarazan gasar karatun Alƙur’ani mai girma a fadar gwamnati da ke Kano.

A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikewa manema labarai a jiya Talata, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa wajen ci gaban karatun Alkur’ani mai girma.

A yayin taron, gwamna Yusuf ya sanar da daukar nauyin karatun gwarazan su biyu, Gwani Sunusi Abubakar mai shekara 17 da Gwana Fatima Abubakar zuwa Jami’ar Al-Azahar da ke Egypt.

KU KUMA KARANTA:Ba a kashe matashi Abdulsalam Rabiu da mahaifinsa ba, sai dai suna hanun ‘yan bindiga – Gwamnatin Katsina

Baya ga haka, ya baiwa su biyun kujerun aikin Hajji da kyautar filaye da kuma kyautar kuɗaɗe.

Gwarazan ƴan asalin jihar Kano ne, inda Gwani Sunusi Abubakar ya fito daga karamar hukumar Gezawa ya samu nasara a matakin kasa tare da Gwana Fatima Abubakar wadda itama ta samu nasara a matakin kasa.

Sauran wadanda su ka zo na biyu da na uku su ma sun samu kyautar Naira miliyan 1 da kujerar aikin Hajji ko wannensu.

Leave a Reply