Gwamnan Kano ya fara biyan ’yan fansho 5,000 hakkokinsu

0
162

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ƙaddamar da biyan naira biliyan biyar daga cikin bashin hakkokin ’yan fansho 5,000 da gwamnatinsa ta gada a jihar.

Gwamna Abba ya ce mutum 5,000 da za a biya hakkokinsu sun haɗa da ’yan fanshon da suka rasu kafin a biya su kuɗaɗen fansho da garatuti daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Ya shaida wa taron fara biyan kuɗaɗen a ranar Asabar cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da biyan hakkokin ’yan fanshon da yawansu ya kai naira biliyan 48.

Abba Gida-gida ya kuma bayyana cewa yankan albashin ma’aikatan jihar da ake yi ba bisa ka’idaba da sunan ɓangarensu na kuɗin fansho, ya zama tarihi.

A jawabinsa, Kwamred Abdullahi Tsohon Garba, wanda ya wakilici Shugaban Ƙungiyar ’yan fansho ta ƙasa (NUP) Kwamred Godwin Abumisi, ya ce abin yawa ne yadda gwamnan ke biyan hakkokin ’yan fansho a daidai lokacin da wasu takwarorinsa gwamnoni suka fi mayar da hankali kan wasu matsaloli a jihohinsu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Zamfara ya jagoranci taron majalisar zartaswar jihar, ya karɓi rahoton kwamitin ‘yan fansho

Ya bayyana cewa biyan hakkokin naira biliyan biyar ya  nuna idan aka ci gaba, nan gaba za a gama biyan duk bashin hakkokin ’yan fansho a Jihar Kano.

A nasu jawaban, Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamred Amimu Abdulsalam da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafizu Abubakar sun shawarci ’yan fanshon da cewa kada su bari albashinsu da gwamnatin baya ta riƙa yankewa da sunan fansho ba bisa ka’ida ba ya tafi a banza.

Sun kuma shawarci ’yan fanshon da su kai ƙara ga hukumomin yaƙi da almundahana domin ganin an ƙwato musu hakkokinsu.

Leave a Reply