Gwamnan Kano ya dakatar da ma’aikata dubu 10, waɗanda Ganduje ya ɗauka aiki

1
218

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da biyan albashin ma’aikata 10,000 da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta ɗauka cikin gaggawa, har sai an gudanar da bincike.

Babban Akanta Janar na jihar Abdulƙadir Abdulsalam ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano ranar Litinin.

Abdulsalam ya ce ma’aikatan da abin ya shafa sun yi aiki ne a tsakar gwamnatin da ta gabata.

Ya ce an kafa wani kwamiti da zai binciki yadda suka shiga cikin ma’aikatan gwamnati, inda ya tabbatar da cewa sakamakon binciken zai taka rawa a cikin makomarsu.

KU KUMA KARANTA: “Idan na saɓa rantsuwar da na yi, babu lauyan da zai kare ni a cikin kabari” – Gwamnan Kano

Akanta Janar ɗin ya kuma sanar da dakatar da sauya sheƙar da gwamnatin da ta gabata ta yi a cikin ma’aikatan gwamnati bisa ƙa’idojin da ake da su, inda ya ƙara da cewa ya kamata jami’an gwamnatin da abin ya shafa su ci gaba da riƙe matsayinsu.

Abdulsalam ya bayyana shirin sabuwar gwamnati na biyan albashin ma’aikata da ranar 25 ga kowane wata, domin ya bayyana cewa za a biya ma’aikatan da suka yi ritaya fansho da gratuity kamar yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana cewa sabuwar gwamnatin za ta yi aiki da asusu guda domin tabbatar da ɗa’a da harkokin kuɗi.

1 COMMENT

Leave a Reply