Gwamnan Kano ya bawa ƙungiyar ‘yan jaridu buhunan shinkafa 450

0
15
Gwamnan Kano ya bawa ƙungiyar 'yan jaridu buhunan shinkafa 450

Gwamnan Kano ya bawa ƙungiyar ‘yan jaridu buhunan shinkafa 450

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf Sanusi Bature D-Tofa ya Sanyawa hannu.

Bature yace kungiyoyin da suka amfana sun hada da kugiyar ƴan jaridu ta ƙasa reshen jihar (NUJ) da kugiyar Jami’an hulɗa da jama’a ta ƙasa reshen jihar Kano (NIPR) da kugiyar mata ƴan jaridu (NAWOJ) da kugiyar maruba labarin wasanni reshen jihar Kano (SWAN) sauran sun haɗa da kugiyar ma.’akatan radio da talavijin da wasan kwaikwayo da kirkira (RATTAWU) da kugiyar shugabannin kafafen ƴaɗa labarai.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Kano, sun kama ‘yan bindiga suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47

Raban ya gudana a cibiyar ƴan jaridu dake gidan gona a jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Comr Ibrahim Abdullahi Waiya da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature D-Tofa da wakilan kafafen ƴaɗa labarai da Kuma kungiyoyin.

Ana saran nan gaba kaɗan sauran kungiyoyin ƴan jaridu zasu karɓi nasu Rabon Idan Allah ya so.

Leave a Reply