Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kwashe illahirin masu larurar ƙwaƙwalwa da ke gararamba a kan titunan jihar a birni da ƙauye.
Alfijir labarai ta rawaito Fauziyya D Sulaiman, hadima ta musamman ga Gwamnan kan harkokin jin-ƙai ce ta shaida hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na facebook a ranar talata.
Ta ce gwamnan ya bada umarnin ne bayan koke-koken da al’umma su ka shigar ga gwamman
Ta ƙara da cewa tuni dai aka fara aikin kwashe masu larurar zuwa asibitlcin masu larurar ƙwaƙwalwa domin kulawa da lafiyar su.
“Bayan koke-koke da aka shigar gurin Gwamnan Abba Kabir Yusuf akan masu larurar kwakwalwa da ke yawo akan titunan Kano cikin birni da ƙauye wasunsu ma tsirara suke yawo, wasu ana cutar da rayuwarsu musamman mata, kuma ba su da galihun da zaa ɗauke su akai su asibiti, mai girma Gwamna ya bayar da umarnin a kwashesu akai su Asibitin masu Larurar kwakwalwa domin kulawa da lafiyarsu.
“Yau muka fara wannan aikin karkashin hukumar Agajin gaggawa (SEMA) da kuma office ɗina, SSA Needy and Valnurble,” in ji ta.