Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero

Published

on

Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero

Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero

Gwamnan Jihar Kano ya ba da umarnin kama Alhaji Aminu Ado Bayero saboda zargin yunƙurin tayar da tarzoma a jihar bayan sanar da sauke shi daga sarautar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ne raanar Asabar da safe ta hannun daraktansa na yaɗa labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Abba Kabir ya ce Aminu Ado “ya shiga Kano cikin daren da ya gabata, don shiga fadar Kano da ƙarfin tsiya kwana biyu bayan sauke shi daga sarauta.”

“Bisa haka ne gwamnan ya ba da umarnin kama tuɓaɓɓen Sarkin nan-take saboda kawo tsaiko a zaman lafiyar al’umma da kuma yunƙurin rusa kwanciyar hankalin da ake da shi a Kano,” a cewar sanarwar.

Ranar Juma’a da tsakiyar dare ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano, daga nan ya zarce Gidan Sarki na Nasarawa, wanda ke da nisan kimanin kilomita ɗaya daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

A ranar Juma’a ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sabon Sarki, kwana ɗaya bayan sa hannu a gyaran dokar Masaratun Kano ta 2024, wacce ta rushe masarautun jihar biyar ta kuma sauke sarakunan jihar, kamar yadda gwamnan ya ce.

A jawabin da ya gabatar ranar Juma’a lokacin miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar a fadar Gwamnatin Kano, Gwamna Abba ya ce Sarki Sanusi zai ci gaba da zama a masaukinsa ana ci gaba da al’umuran sarauta, har zuwa wani lokaci.

Sai dai ranar Juma’a da tsakar dare Sarki Sanusi II ya shiga fadar ta Kano bisa rakiyar tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa da shugaban majalisa da wasu ƙusoshin gwamnati.

Matakin ya biyo bayan raɗe-raɗin cewa Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin komawa Kano sannan ya shiga Gidan Sarauta, kamar yadda Mataimakin Gwamnan Jihar Kwamared Aminu Abdussalam ya sanar da safiyar Asabar.

Ya yi gargaɗin cewa za su ɗauki duk wani mataki na ganin cewa naɗin da aka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II ya tabbata.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II Sarautar Kano

Mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake zanta wa da ‘yan jarida da safiyar Asabar a fadar Masarautar Kano.

Ya zargi wasu da ke kusa da gwamnatin tarayya da yin amfani da jami’an tsaro wajen “ganin cewa an tanƙwara an banƙara a kan buƙatar al’ummar jihar Kano an kawo musu abin da ba shi suke buƙata ba.”
“Wannan shi ne abin da ya kawo mu yau.”

“Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya karɓi takardarsa ta kama aiki, kuma muna kawo shi nan gidan, muna zagaya gidan da shi,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan jarida a fadar Sarkin Kano.

Ya ƙara da cewa duk wasu manya na gwamnati Kano suna fadar Sarki, kuma za su kasance a fadar har sai komai ya daidaita.

“Gwamna ne ma gaba ɗaya da gwamnati muka zo muka rako Mai Martaba Sarki da shugaban majalisar da ‘yan majalisa,” in ji shi.

Ya zargi waɗanda suke son mayar da Sarki Aminu da yunƙurin dagula al’amura a Kano.
“Mun kasa gane me ake so a yi… a ɓata duk abin da za a ɓata… saboda ba jihar su ba ce?

Sai dai har kawo yanzu babu wani martani daga gwamnatin tarayyar ƙasar kan abin da ke faruwa a Kano da kuma zarge-zargen gwamnatin ta Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like