Gwamnan Jigawa ya kori Kwamishina kan zargin lalata da matar aure
Daga Ibraheem El-Tafseer
Jami’an hukumar Hisbah a Kano sun kama Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara, bisa zargin yin lalata da wata matar aure.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wanda ake zargin ya shiga hannu ne bayan mijin matar ya kai rahoto ga Hisbah yana zargin kwamishinan da yin alaƙa da matarsa.
Wata majiya a hukumar Hisbah wanda ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa wanda ake zargin har yanzu yana tsare a Hedikwatar Hisbah dake Kano.
Majiyar ta ƙara da cewa bayan samun rahoton, Hisbah ta tura tawagarta ta leƙen asiri don bin diddigin waɗanda ake zargin don tabbatar da gaskiyar batun.
“Mun ɗauki lokaci muna bin diddigin waɗanda ake zargin har sai jiya (Alhamis) da daddare, kimanin ƙarfe 10:00 na dare, lokacin da muka hango wanda ake zargi da matar suna shiga wani gini da ba a kammala ba wanda yake mallakin shi.
KU KUMA KARANTA: An kama wani matashi a Adamawa kan lalata taransifoma
“Da muka ƙarasa wajen ginin, mun buga ƙofar, wanda wani mai gadi ya ke tsare da wajen. Da muka ci gaba da buga ƙofar, wanda ake zargin da kansa ya fito don ganin suwaye ke ƙofar.
“Da ya buɗe kofar, muna tare da mijinta wanda ya shigar da ƙarar kuma ya gan ta a cikin mota,” inji majiyar.
Majiyar ta ƙara da cewa da ta ga mijinta tare da jami’an Hisbah, sai ta firgita kuma ta yi ƙoƙarin tserewa a cikin motar, inda ta cire ƙyauren gidan amma tana fita waje ta tarar da motar Hisbah ta toshe ƙofar wucewa.
Majiyar ta ce kwamishinan ya amsa laifin yin lalata da matar har sau uku.
Majiyar ta ƙara da cewa an tsare su biyun a Hedikwatar Hisbah kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Da aka tuntuɓi Mataimakin Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen, domin jin ta bakinsa, bai amsa wayar wakilinmu ba kuma bai mayar da saƙon kar ta kwana ba wajen ba da amsa kan lamarin.
Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan ya fitar a yau Asabar ya musanta zargin cewa an kama shi yana lalata da matar aure, inda yayi barazanar kai batun gaban kotu.
A halin yanzu kuma, Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya sanar da dakatar da kwamishinan har sai an kammala bincike.