Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata, ya bayar da umarnin rusa gidajen karuwai da masu aikata laifuka da suka yi ƙaurin suna wajen karuwanci, ’yan daba da sauran miyagun ayyukan cikin sa’o’i 72.
Zulum ya ba da umarnin ne a wata ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru a ‘Bayan Quarters’, wani matsugunin da ke kusa da rukunin gidajen ma’aikatan jirgin ƙasa, a Maiduguri.
Yankin yana ɗaukar ‘yan daba, ayyukan aikata laifuka da ƙananan yara don karuwanci na kasuwanci.
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun yawaitar ayyukan ta’addanci da ke da alaƙa da waɗannan haramtattun gidajen karuwai da wuraren aikata laifuka da suka haɗa da karuwanci da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan haram.
KU KUMA KARANTA: An rushe gidajen karuwai da na rawar gala a Yobe
Ya ƙara da cewa, waɗannan ayyuka ba wai barazana ce ga tsaron jihar kaɗai ba, har ma suna haifar da munanan ɗabi’u da ke lalata rayuwar al’umma da kuma mutuncin ɗaiɗaikun mutane da lamarin ya shafa.
Zulum ya bayyana cewa, yayin da za a rushe matsugunin da ke ɗauke da masu aikata laifuka da ƙananan yara mata domin yin lalata a cikin sa’o’i 72, dama gidajen karuwai ba bisa ƙa’ida ba, Gwamnan ya ba da awanni 12 su fice daga yankin.