Gwamnan Bauchi ya naɗa Alhaji Haruna Ɗanyaya a matsayin sabon Sarkin Ningi
Daga Idris Umar, Zariya
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da naɗin Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a matsayin sabon sarkin masarautar Ningi na 17 a kan mataki sarki mai daraja ta 1.
Bincike ya nuna cewa shi dai sabon sarkin Ningi, Haruna Yunusa, an haifeshi ne a shekarar 1956. Kafin masa wannan naɗin shi ne Chiroma Ningi, kuma yana da aure da ‘ya’ya.
Idan za a tuna dai a ranar Lahadi da ta gabata ne Sarkin Ningi, Alhaji (Dakta) Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu yana da shekara 88 a duniya bayan ya mulki masarautar na tsawon shekaru 46 masu albarka.
Naɗin sabon sarkin na ƙushe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barisya Ibrahim Muhammad Kashim ya sa yawa hannu.
A cewar wasiƙar, wannan matakin an ɗauke shine bisa dogara da karfin iko da aka bai wa gwamnan kan doka Cap. 24 Item 3 (1) na dokokin jihar Bauchi kan naɗin sarakuna ta 1991 kuma bayan shawarar da masu alhakin zaɓin sabon sarkin suka bayar a daidai wannan lokacin.
KU KUMA KARANTA:Mai martaba sarkin Ningi ya rasu
A sanarwar manema labarai ɗauke da sanya hannun hadimin gwamnan Bauchi kan yaɗa labarai Mukhtar Mohammed Gidado, da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, gwamnatin jihar ta nuna kwarin guiwarta na cewa sabon sarkin zai ɗaura daga inda mahaifinsa ya tsaya na kyautata zaman lafiya, da haɗin kai da cigaban masarautar Ningi, jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta ce gwamnan jihar ya nanata aniyarsa na cigaba da mara wa sarakunan gargajiya baya domin tabbatar da cigaban jihar a kowani lokaci.
Gwamnan jihar Bala Mohammed ya yi addu’ar Allah dafa wa sabon sarkin ya kuma jiƙan Marigayin babansa.
A yayin da ke taya sabon sarkin murna, ya masa fatan samun lafiya da kuma fatan yin mulki cikin nasara.