Gwamnan Bauchi ya jajanta wa majalisar jihar, bisa ga rasuwar ɗaya daga cikinsu

0
310

Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar Bauchi ya jajantawa ‘yan uwa da abokan arziƙi da ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi bisa rasuwar ɗan majalisa Ado Wakili.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnatin jihar Bauchi, Suleman Dambam, ya fitar ranar Lahadi.

KU KUMA KARANTA: Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa jihar Yobe Lawan Gana, ya rasu

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta bayar da rahoton cewa Wakili, memba mai wakiltar mazaɓar Burra ta karamar hukumar Ningi a jihar, ya rasu ne a ranar 16 ga watan Yuni, kwana uku da kammala aikinsa bayan gajeruwar rashin lafiya.

Bala Mohammed ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi, ba ga al’ummar mazaɓar Burra kaɗai ba, ga sauran takwarorinsa na majalisar dokokin jihar da ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi.

Ya ce za a iya tunawa ɗan majalisar bisa ga irin gudumawar da ya bayar a fagen siyasar jihar Bauchi, musamman a matsayinsa na ɗan majalisa.

Gwamnan ya buƙaci ‘yan uwa da abokan arziƙi da kuma ’yan mazaɓarsa da ya wakilta kuma ya yi wa aiki a rayuwarsa, da su tabbatar da cewa abin da ya bari ya ɗore.

“A madadin iyalaina da gwamnati da kuma al’ummar jihar Bauchi, ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga iyalansa da kakakin majalisar jihar da ɗaukacin ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi baki ɗaya.

“Ina kuma miƙa ta’aziyyata ga Masarautar Ningi da ɗaukacin al’ummar Jihar Bauchi.

“Ina ƙira gare ku da ku jure wannan rashi da ƙarfin gwiwa tare da yin addu’a Allah ya karɓi ransa, ya jajanta wa masoyansa, ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi.”

Hakazalika, kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya kuma bayyana kaɗuwarsa bisa rasuwar ɗan majalisar wanda ya bayyana a matsayin ɗan uwa, amintaccen abokin aiki, dattijo kuma uban kowa a majalisar.

Ya ce rasuwar ta sa ta taɓa da kuma raunata dukkanin ‘yan majalisar da ma’aikatan majalisar, inda ya ce shi mutum ne mai matuƙar daraja, tawali’u da barkwanci, wanda duk da shekarunsa ya ɗauki kowa a matsayin aboki.

“Mun yi rashin uba, abokin aiki kuma babban abokin tarayya a daidai lokacin da mazaɓarsa da mai martaba da jiha suka fi buƙatar gudumawarsa.

“A madadin ‘yan uwa da ma’aikatan gidan, ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga iyalansa, mutanen mazaɓar Burra da ƙaramar hukumar Ningi,” inji shi.

Leave a Reply