Gwamnan Bauchi ya amince da ɗaukar ma’aikata 1,684

1
326

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya amince da ɗaukar ma’aikata sama da 1,684 a ma’aikatu da hukumomi daban-daban a faɗin jihar.

Shugaban ma’aikatan gwamnati na jiha Alhaji Yahuza Haruna ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan wannan ci gaban ya ce ya ƙunshi ɗaukar malamai 1,000 da suka haɗa da Ingilishi da Lissafi da Biology da Chemistry da Physics da ICT da kuma ma’aikata 154 a Kwalejin Ilimi ta Aminu Saleh dake Azare.

Haruna ya ci gaba da cewa, gwamnan ya kuma amince ma’aikatar aikin gona ta ɗauki ma’aikatan ƙarafa da manajojin gona 206.

KU KUMA KARANTA: Muna da ɗalibai 350, amma malamai uku kacal muke dasu – Al’ummar Gabchyari ta jihar Bauchi

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan sanarwar ɗage takunkumin da Gwamna Mohammed ya sanyawa hannu ne a jawabinsa na ƙaddamarwar a ranar 29 ga watan Mayu a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa Bauchi.

Shugaban ma’aikatan ya yabawa gwamnan bisa wannan karimcin tare da bayyana fatan ganin wannan aikin zai samar da ma’aikatan da ake buƙata a sassan da suka dace da kuma bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Don haka ya gargaɗi masu buƙatar da su yi hattara da masu damfara yana mai jaddada cewa gwamnati da jami’an tsaro za su sanya ido kan lamarin da nufin zaƙulo masu laifi.

1 COMMENT

Leave a Reply