Gwamna Zulum ya sake naɗa mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, da wasu 11

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya sake naɗa Malam Isa Gusau a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru.

Haka kuma gwamnan ya naɗa wasu goma sha ɗaya a matsayin manyan mataimaka na musamman da manyan manajoji da sakatariyar zartarwa.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa Gusau ya yi aiki da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima a lokacin yana gwamnan jihar Borno kafin ya ɗauki irin wannan naɗin da Zulum a zamaninsa na farko.

Haka kuma gwamnan ya sabunta naɗin na Hon. Baba Shiekh Haruna a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai; Hon. Abdul Rahman Ahmed Bundi a matsayin babban mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yaɗa labarai.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya ba da umarnin a binciki likitocin da suka ƙi karɓar mutanen da suka yi hatsarin mota

Ya kuma naɗa Ambasada Adamu Abbas a matsayin babban manazarci kuma mai bincike; Hon Injiniya Baba Bukar Gujbawu, mai ba da shawara na musamman kan sa ido da tantancewa da Dakta Mairo Mandara a matsayin babbar mai ba da shawara kuma mai gudanarwa, ci gaba mai ɗorewa, haɗin gwiwa da tallafin jin ƙai.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Hon. Ahmed Sanda – mai ba da shawara na musamman kan yarjejeniya; Injiniya Ibrahim Idris a matsayin mai ba da shawara na musamman, ayyuka na musamman; Hon. Ibrahim Dangana (Relay) – mataimaki na musamman kan Protocol; Hon. Umar Mohammed a matsayin babban manaja, gidan rediyon Borno (BRTV); Dakta Babakura Mamman Gadai a matsayin babban sakataren hukumar raya ci gaba ta jihar Borno, haɗin gwiwa da bayar da agajin jin ƙai, sai kuma Liman Gana Mustapha a matsayin babban manajan hukumar tsara birane da raya birane ta jihar Borno.

Wata sanarwa da Barista ya raba wa manema labarai ranar talata a Maiduguri.

Mustapha Ali Bogusuma, babban sakataren gwamnati ya bayyana cewa Gwamna Zulum ya yi waɗannan naɗe-naɗen ne bisa la’akari da cancanta da kuma bayanan shekarun baya a aikin gwamnati.


Comments

One response to “Gwamna Zulum ya sake naɗa mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, da wasu 11”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya sake naɗa mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, da wasu 11 […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *