Gwamna Zulum ya canza sunan jami’ar jihar Borno zuwa jami’ar Kashim Ibrahim
Daga Ibraheem El-Tafseer
Majalisar zartaswar jihar Borno ta amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Borno (BOSU) zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri, domin karrama Sir Kashim Ibrahim, Gwamnan Arewacin Najeriya na farko.
An ɗauki matakin ne a yayin zaman majalisar na farko a shekarar 2025, wanda Gwamna Babagana Zulum ya jagoranta a Maiduguri.
Da yake zantawa da manema labarai a kan lamarin, kwamishinan yaɗa labarai da tsaro na cikin gida, Farfesa Usman Tar, ya ce sauya sunan zai fara aiki ne bayan gyara da kuma sanar da hukumomin da suka dace.
“Majalisar ta amince da cewa Jami’ar Jihar Borno za ta koma Jami’ar Kashim Ibrahim.
“Wannan shawarar ta bi matakan doka da Majalisar dokoki ta jihar ta yi don gyara dokar kafa jami’ar da ayyukan da ma’aikatar ilimi ta yi don sanar da hukumomin da abin ya shafa kamar NUC da JAMB,” in ji Tar.
Ya ce majalisar ta amince da wani gagarumin shiri na sanya sunayen gidaje da lambobin gidaje a cikin garin Maiduguri da sauran garuruwa a wani ɓangare na kokarin sabunta biranen jihar.
Tar ya bayyana cewa shirin zai ƙunshi haɗa hannu da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarakunan gargajiya da hukumomin tarayya irin su ma’aikatan gidan waya ta Najeriya.
Tun da farko a lokacin da yake jawabi ga ‘yan majalisar, Zulum ya nuna jin daɗinsa kan jajircewarsu tare da bayyana tsare-tsaren ƙarfafa ƙoƙarin farfaɗo wa da aiwatar da ayyuka masu tasiri a shekarar 2025.
KU KUMA KARANTA: Miji da mata sun zama farfesoshi a lokaci guda a jamiar Bayero
“A shekarar 2024, gwamnatina ta samu ci gaba sosai, kuma na ƙuduri aniyar ganin na ƙara samun nasarori a wannan shekarar.
Zulum ya ce “Mayar da hankalinmu zai ci gaba da kasancewa kan farfaɗowar jihar bayan rikice-rikice, da sabunta birane, da kyautata jin daɗin ‘yan ƙasa.”