Gwamna Yusuf ya amince da sayen taki na naira biliyan 5 don manoman Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sayan taki na kimanin Naira biliyan 5.07 domin tallafawa ƙananan manoma a jihar.
Wannan yunƙuri na da nufin sauƙaƙa wadatar abinci a matsayin sabon tsarin ci gaban noma a jihar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano a yau Talata, an ba da amincewar ne yayin taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 15, SEC.
“Za a raba takin ne a faɗin ƙananan hukumomi 44 domin tallafa wa manoma musamman na karkara domin ƙara yawan amfanin gona a kakar damina ta 2024,” inji shi.
KU KUMA KARANTA: Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano
Ya bayyana cewa za a sayar wa manoman takin ne a kan farashi mai rahusa, wanda hakan ke nuna aniyar gwamnan na samar da kayan amfanin gona masu inganci da araha.
Wannan matakin ya biyo bayan siyan hatsi na biliyoyin nairori a baya da gwamnan ya yi, inda aka raba wa marasa galihu a jihar domin rage raɗaɗi.