Gwamnan Yobe zai ƙaddamar da sabon shirin tallafin noma na bana (Hotuna)

0
256
Gwamna Yobe zai ƙaddamar da sabon shirin tallafin noma na bana
Gwamnan Yobe Hon. Dakta Mai Mala Buni

Gwamnan Yobe zai ƙaddamar da sabon shirin tallafin noma na bana

A wani yunƙuri na ci gaba da bunƙasa harkar noma da ƙarfafa gwiwar manoma a karkara, Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji (Dr.) Mai Mala Buni, CON, zai ƙaddamar da wani sabon Babban Shirin Tallafin Noma domin kakar noman shekarar 2025.

Za a gudanar da wannan muhimmiyar ƙaddamar wa a gobe Talata, 29 ga Yuli, 2025 a filin wasa na August 27 Stadium da ke Damaturu, da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Wannan sabon shiri na bana yana ci gaba ne da matakin da Gwamna Buni ya dauka a bara, inda ya kaddamar da babban shirin tallafin noma mai darajar naira biliyan 14 (₦14bn) domin bunkasa samar da abinci, samar da ayyukan yi da kuma karfafa zaman kace wando ga al’ummar jihar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin Tafkin Chadi

Shirin bana na 2025 zai kara daukaka wannan tsari, inda za a raba sabbin kayan aikin noma, traktoci, taki, injinan noma na hannu don karfafa noma na zamani a cikin kananan hukumomi 17 na jihar.

Gwamnatin Gwamna Buni na ci gaba da jajircewa wajen inganta noma a matsayin ginshikin tattalin arziki, ci gaban karkara, da rage talauci, musamman a wannan lokaci da kasar ke fuskantar kalubalen rashin wadataccen abinci.

Leave a Reply