Gwamna Uba Sani ya ziyarci ɗaliban makarantar Kuriga da aka sako (Hotuna)

0
58
Gwamna Uba Sani ya ziyarci ɗaliban makarantar Kuriga da aka sako (Hotuna)

Gwamna Uba Sani ya ziyarci ɗaliban makarantar Kuriga da aka sako (Hotuna)

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ziyarci makarantar firamare da ƙaramar sakandire ta LEA da ke Kuriga a ƙarshen makon da ya gabata, inda ya samu kyakkyawar tarba daga ɗalibai, malamai, da sauran jama’ar gari.

Neptune Prime Hausa ta rawaito cewa, a ranar 24 ga watan Maris, 2024, ‘yan bindiga sun sace ɗalibai sama da 180 kuma suka sami ‘yancinsu bayan makonni biyu da aka yi garkuwa da su.

A ziyarar tasa Gwamna Sani ya tattauna kai tsaye da daliban, inda ya tattauna da ɗaliban da suka samu ‘yanci tun dawowar su da kuma ci gaban da suka samu a makarantar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

Ɗaliban sun ba da amsa mai kyau da ban sha’awa, tare da nuna godiya ga ‘yancinsu da tallafin da suka samu.

Gwamna Sani ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da tsaron ɗaliban, inda ya ce, “Za mu yi duk mai yiwuwa don ganin kun koyi karatu a cikin yanayi mai aminci da tsaro.”

Gwamnan ya kuma duba aikin gyaran makarantar da aka yi a baya-bayan nan, wanda aka inganta da kayan aiki na zamani

Sannan ya nuna gamsuwa da ingancin aikin, tare da lura da cewa an aiwatar da shi ne bisa ƙayyadaddun ayyuka da ma’auni.

An dai ɗauki ziyarar a matsayin wani gagarumin ƙwarin gwiwa ga ɗaliban, waɗanda suka tsallake rijiya da baya,bayan a sace su, kuma yanzu sun mayar da hankali kan karatunsu.

Ga hotunan ziyarar:

Leave a Reply