Gwamna Legas ya yi ƙira ga masu zanga-zanga a jihar da su zo su tattaunawa

0
73
Gwamna Legas ya yi ƙira ga masu zanga-zanga a jihar da su zo su tattaunawa

Gwamna Legas ya yi ƙira ga masu zanga-zanga a jihar da su zo su tattaunawa

Daga Ali Sanni

Gwamnan jihar Legas, Babatunde Sanwo Olu, ya yabawa masu zanga-zanga a jihar gami da yadda suka gudanar da Zanga-zangar cikin lumana da kuma dakatar da zanga-zanga sakamakon jawaban da shugaban ƙasar yayi a safiyar Lahadi.

Gwamna Sanwo-Olu ya yabawa shuwagabannin zanga-zangar a jihar tasa, inda ya ƙara da cewa dakatar da zanga zangar da sukayi alamune na nuna cewa sun gamsu da cewa shugaban ƙasar yaji koken su. Yace hakan ya nuna cewa su wayyayun matasa ne.

Dan nuna damuwa da kuken matasan, gwamnan yace zai cigaba da tattaunawa da matasan domin biya musu buƙatunsu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Gombe sun kama mutum 90 kan zargin sace kayan jama’a a lokacin zanga-zanga

Sanwo-Olu ya shawarci ministan matasa dana tasirin cigaban al’umma, dana yaɗa bayanai da wayar da kan al’umma da su buɗe ƙofar tattaunawa da masu zanga-zangar dan warware matsalolin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here