Gwamna Lawan ya amince da naira biliyan huɗu don gyara hanyoyi a Gusau

0
283

Gwamna Dauda Lawan na Zamfara ya amince da naira biliyan 4 don gyara hanyoyin cikin Gusau a matakin farko.

Jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ayyuka da sufuri, Idris Mainasara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Alhamis.

Idris Mainasara mai ba da shawara na musamman kan samar da ababen more rayuwa da raya birane, Ibrahim Agege ya sanar da cewa an bayar da kwangilar ne ga kamfanin Ronchess Global Resources PLC.

KU KUMA KARANTA: Hukumar CSDA ta horar da ma’aikata 886 a Zamfara

Hanyoyin da ake sa ran za a gyara sun haɗa da Bello Barau daura da ofishin ‘yan sanda na Gusau, Bello Barau daura da gidan gwamnati, Bello Barau daura da Tsohuwar Kasuwa, Junction ‘yan Kekuna, fadar sarki da Rankin Ruwa duk a cikin birnin Gusau.

Don haka gwamnatin jihar ta nemi goyon baya da haɗin kan mai martaba Sarkin Gusau Ibrahim Bello domin wayar da kan mutanen da ayyukan ya shafa.

Leave a Reply