No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan Kano ya yi gargaɗi mai zafi ga ma’aikatan gwamnatinsa, bayan Namadi ya yi murabus

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya fitar da gargaɗi mai tsanani ga dukkan jami’an gwamnati bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, wanda ya yi murabus biyo bayan cece-kuce kan belin wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na 30 da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Laraba.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani hali da zai lalata ƙimar da ta gina ba, yana mai cewa duk jami’in da ya kasa riƙe amana ya fi dacewa da ya ajiye aikinsa.

KU KUMA KARANTA: Belin dilan ƙwayoyi a Kano, Gwamna Abba ya Umurci a yi bincike kan zargin da hannun kwamishinan Sufuri

Ya ce yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran munanan dabi’u na daga cikin ginshiƙan gwamnatinsa, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu kai tsaye ko a kaikaice wajen irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukunci.

Gwamnan ya kuma yi kira ga masu rike da mukamai su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, rikon amana da kima, domin kare mutuncin gwamnatin da suke wakilta.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...