Gwamna Buni zai gina kantin sayayya ‘City Mall’ a Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya ɗauki azamar sauya fasalin babban birnin jihar Yobe, wato Damaturu, wajen gina katafaren kantin sayar da kayayyakin alatu na zamani mai suna ‘City Mall’ a ƙoƙarin sa na bunƙasa harkokin yawon buɗe-ido tare da samar sabbin hanyoyin ci gaban tattalin arziƙin jihar.

Wannan sabon katafaren Kantin ‘Yobe City Centre’ wata sabuwar fuskar kasuwanci ce a jihar Yobe, inda ‘yan jihar zasu rinƙa samun kowane nau’in kayayyakin buƙatun yau da kullum kamar mutum ya na birnin Dubai da makamantan su a faɗin duniya.

Aikin, idan an kammala shi, zai zama abin alfahari na zamani ga al’ummar jihar Yobe; zai ƙunshi shagunan sayar da kayayyaki, wuraren nishaɗi, shaƙatawa, da na cin abinci, tare da maka-makan shagunan sayar da kayayyaki, da sauran ƙayatattun wurare gwanin sha’awa, wanda za su mayar da Damaturu hamshaƙin babban birni na zamani.

Ana sa ran mazauna birnin Damaturu, waɗanda suka kasance suna cin kasuwa a cikin cunkoson Bayan Tasha, za su ci gajiyar more wannan sabon Kantin sayayya na zamani cikin kyakkyawan tsari mai nagarta.

KU KUMA KARANTA: Jihar Yobe ta cika shekaru 32 da zama jiha

A shekaru da dama da suka gabata, ana yiwa jama’ar mu shaguɓen cewa a matsayin Damaturu babban birnin jihar Yobe, amma ba shi da kasuwannin zamani, ballantana manyan kantuna da shagunan sayayya na zamani irin biranen Kano ko Abuja wajen sayayyan kayan alatu na zamani, al’amarin yanzu kaya ya tsinke a gindin kaba; Gwamna Buni ya ɗaura aniyar sauya fasalin kallon da sauran al’ummar ciki da wajen jihar ke yiwa Damaturu.

Sakamakon haka ya dace mu ci gaba da marawa gwamnatin Buni baya wajen ganin wannan aiki ya tabbata. Saboda abubuwan da wannan katafaren Kantin zai samar bai gaza irin wanda takwarorinsa a Turai, Dubai ko sauran wurare ke samarwa ba. Bayan kammala aikin, zai ƙarawa kasuwar Damaturu Ultra-Modern Market ƙarfi, kuma babu sauran zuwa sayayya a Shoprite Kano ko Abuja.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *