Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Alhaji Mai Mala Buni CON, ya yiwa takwaransa na jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ta’aziyya bisa ga rasuwar mai magana da yawunsa Malam Isa Gusau.
A wata takardar manema labarai, da babban daraktan yaɗa labarai na Gwamna Buni ya fitar, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce, Gwamna Buni ya bayyana Gusau a matsayin jami’i mai ƙwazo wanda ya yi wa mai gidansa hidima da jajircewa da kuma dagewa a wajen aiki.
“Gusau ya ƙware wajen sarrafa bayanai a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a yankin Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno.
“Za a tuna da shi bisa jajircewarsa, da ƙoƙarinsa wajen gudanar da ayyuka, da kuma tsawon shekaru da ya yi yana yi wa gwamna da gwamnatin jihar Borno hidima,” in ji Gwamna Buni.
KU KUMA KARANTA: Mai magana da yawun gwamna Zulum, Isa Gusau, ya rasu
“Ina miƙa ta’aziyya ga mai girma ɗan’uwa na Gwamna Zulum, gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa wannan rashi da aka yi a daidai lokacin da ake buƙatar ayyukansa don tallafa wa gwamnati.” Inji Gwamna Buni.
Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma baiwa iyalansa haƙurin jure wannan rashi.
Gusau ya taɓa zama mai baiwa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima shawara kan harkokin yaɗa labarai a lokacin yana gwamnan jihar Borno kuma Gwamna Zulum ya ci gaba da tafiya da shi, wanda ya shafe kimanin shekaru biyar yana mulki.