Gwamna Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙar ambaliyar ruwa a jihar

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON,  ya umurci ma’aikatun ayyuka da muhalli na jihar da su ƙara ƙaimi don duba yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗi.

Gwamnan ya ce dole ne a ƙara tsaurara matakan da aka ɗauka tun da farko, saboda yawan ruwan sama a jihar nan ba da jimawa ba zai yawaita.

Ya kuma umurci ma’aikatun da abin ya shafa da hukumominsu da su tuntuɓi ofishin sakataren gwamnatin jihar domin ɗaukar matakan da za su rage ambaliyar ruwa yadda ya kamata.

“Dole ne matakan su kasance masu inganci da daidaito don rage ambaliyar ruwa yadda ya kamata da kuma kare al’ummominmu.

KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA

“Gwamnati ta himmatu wajen samar da kayan aiki da ake buƙata domin daƙile wannan matsala.

Gwamna Buni ya ce “Gwamnati za ta haɗa al’ummomin da ke fama da ambaliyar ruwa domin yaƙi da ambaliyar ruwa.”

Sai dai ya yi ƙira ga jama’a da su ba gwamnati haɗin kai da shawarwarin ƙwararru da aka ba su don tabbatar da tsaron lafiyarsu.

“Mutanen mu mazauna birane su ma su tallafa wa gwamnati ta hanyar share magudanan ruwa a gaban gidajensu.

“Ya kamata ku guji yin gine-gine don toshe magudanan ruwa domin kawo cikas da ambaliya a cikin gidajenku da sauran su” Gwamnan ya shawarci.

Gwamna Buni ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta shirya tsaf domin tunkarar matsalar da ke iya faruwa.


Comments

2 responses to “Gwamna Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙar ambaliyar ruwa a jihar”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙar ambaliyar ruwa… […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙar ambaliyar ruwa… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *