Gwamna Buni ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON (Chiroman Gujba) ya amince da rushe shugabannnin dukkanin ƙananan hukumomin jihar guda 17, biyo bayan ƙarewar wa’adinsu na ofis a wannan watan na Mayu.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Baba Mallam Wali mni, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata takarda da ya saka wa hanu.

KU KUMA KARANTA: Yobe ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda

“Shugabannin, za su miƙa al’amuran ƙananan hukumominsu ga daraktocin kula da ma’aikata na ƙaramar hukumar.

“Gwamna Buni ya ƙara nuna godiyarsa ga shugabannin riƙo ɗin, bisa goyon bayansu, jajircewarsu da nasarori daban-daban da aka samu a lokacin aikinsu.


Comments

One response to “Gwamna Buni ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar Yobe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar Yobe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *