Gwamna Yobe ya amince da naɗa Abdullahi Musa Shehu a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jihar
Gwamnan jihar Yobe Hon. (Dr.) Mai Mala Buni CON ya amince da naɗin Abdullahi Musa Shehu a matsayin shugaban ma’aikatan jihar Yobe na riƙo.
KU KUMA KARANTA: Ranar Ma’aikata: Ƙungiyar ƙwadago ta sha alwashin inganta jin daɗin ma’aikatan jihar Yobe
Kafin a naɗa shi, shi ne sakataren dindindin na ma’aikatar ayyuka a jihar. Kuma zai kama aiki nan take daga naɗin nasa.









