Gwamatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da ambaliya

0
70
Gwamatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da ambaliya

Gwamatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da ambaliya

Daga Idris Umar, Zariya

A jiya Laraba ne ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Farfesa Joseph Terlumun Utsev, ya ƙaddamar da wani kwamitin ƙwararru da zai samar da dabarun daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar nan.

Kwamiti zai yi aikin samar da taswirar inganta madatsun ruwa da tsarin zamantakewa da ma wasu ƙarin shirye-shiryen inganta muhalli cikin gaggawa.

Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu muhimman tsare-tsare guda biyu da suka haɗa da kafa asusun bayar da agajin Ibtila’i da samar da kwamitin yaƙi da ambaliya ruwa .

KU KUMA KARANTA: Matafiya sun maƙale bayan ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wani gada

Waɗanda suka halarci taron ƙaddamar da kwamitin sun haɗa da; Ministan Watsa Labarai, Muhammad idris da na Kasafin Kuɗi, sanata Abubakar Atiku Bagudu, da Ministar Muhalli, Balarabe Abbas, inda dukansu suka jaddada buƙatar ganin kwamitin ya fara aiki nan take.

Kazalika gwamatin Shugaba Tinubu ta ware kuɗaɗen tallafin yaƙi da Ibtila’in ambaliyar ga ilahirin jihohin ƙasar.

Wannan matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen shawo kan iftila’in ambaliyar ruwa da samar da kariya ta dindindin a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Ana tunanin hakan zai taimaka wajen magance iftila’in ambaliyar ruwa a nan gaba.

Leave a Reply