Guguwa mai ƙarfi ta kashe mutane 11 a Pakistan

Wata mahaukaciyar guguwa mai ƙarfin gaske ta kashe aƙalla mutane 11 daga wata ƙabilar makiyaya ciki har da wani yaro ɗan shekara huɗu suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwa a arewacin Pakistan.

Dusar ƙanƙara ta faɗo a lokacin da ƴan ƙungiyar suka tsallaka wani yanki mai tsaunuka tare da garken awakinsu.

An kuma samu jikkatar wasu mutane 25, inda ake ci gaba da aikin ceto.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya bayyana alhininsa game da mutuwar mutanen, inda ya ce al’amura irin su ƙanƙara na ƙaruwa saboda sauyin yanayi.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya auku ne da sanyin safiyar ranar Asabar a wani ɓangare na hanyar da ta bi ta gundumar Astore na yankin Gilgit Baltistan zuwa maƙwabciyarta Azad Kashmir, a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Pakistan.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama ya kashe mutane 7, ya raunata da dama a Delta

Wasu mata huɗu da yaro ɗan shekara huɗu na daga cikin waɗanda suka mutu, kamar yadda babban jami’in ‘yan sanda Ziarat Ali, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Jami’an aikin ceto sun fuskanci ƙalubale saboda nisa da kuma wahalar zuwa da yankin yake da shi.


Comments

3 responses to “Guguwa mai ƙarfi ta kashe mutane 11 a Pakistan”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Guguwa mai ƙarfi ta kashe mutane 11 a Pakistan […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Guguwa mai ƙarfi ta kashe mutane 11 a Pakistan […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *