Gobara ta tashi a matatar man Ɗangote
Gobara ta tashi da yammacin yau a wani sashe na matatar man Ɗangote da ke kusa da Lekki a Legas.
Jami’an agajin gaggawa sun ɗauki matakin shawo kan lamarin, kuma a cewar rahotannin farko, ba a samu raunuka ba.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano girman barnar da aka yi da kuma abin da ya haddasa faruwar lamarin.
Da take mayar da martani kan gobarar a cikin wata sanarwa da Ɗangote ya fitar, mai ɗauke da sa hannun Anthony Chiejina, ƙungiyar ta ce, “Mun yi gaggawar shawo kan wata ‘yar karamar gobara a masana’antar sarrafa iska (ETP), a yau Laraba 26 ga watan Yuni.
KU KUMA KARANTA: Gobara ta kashe jarirai shida a Indiya
“Babu wani dalili na tashin hankali yayin da matatar ta ke aiki kuma babu wani rauni da aka samu ko lahani ga dukkan ma’aikatanmu da ke bakin aiki.”
Matatar dangote wani katafaren aiki ne da ake ginawa wanda ake hasashen zai iya tace ganga 650,000 a kowace rana.