Girgizar ƙasa ta kashe mutane fiye da 100 a Nepal

0
194

Hukumomi a Nepal sun ce girgizar ƙasa ta kashe mutane aƙalla 130 a Yammacin ƙasar.

An tura jami’an tsaro wurin da lamarin ya faru a yankin Jajarkot, mai nisan kilomita 500 daga Yammacin Kathmandu.

Girgizar ƙasar ta faru ne a tsakar dare, kuma ta fi shafar yankin Jarjarkot wanda bai wuce nisan kilomita 500 ba daga Ktahmandu babban birnin ƙasar.

Mutanen sun riƙa fita daga gidajen su cikin ɗimuwa, kuma hotunan da kafafen yaɗa labaran ƙasar suka fitar sun nuna yadda gidaje suka ruguje.

Ma’aikatan jinya sun ce suna kula da mutane fiye da 40 da aka ceto daga ɓaraguzan gidajen su da suka rushe.

Ƙaramin yanki ne girgizar ƙasar ta faru, kuma ana ci gaba da samun bayanai kan yawan mutanen da suka mutu da kuma aikin ceto.

KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa mai karfin gaske ta kashe mutane 296 a Maroko

An samu ƙarin girgizar ƙasa uku da suka faru a yankin jim kaɗan bayan wannan, inda mutane suka ƙauracewa gidajen su don tsoron abin da zai iya faruwa.

Daga cikin yankunan da aka jiyo girgizar ƙasar dai harda birnin Delhi na ƙasar India.

Nepal ta yi fama da mummunar girgizar ƙasa a shekarar 2015, inda mutane aƙalla dubu tara suka mutu, wasu da dama kuma suka samu rauni.

Leave a Reply