Girgizar ƙasa ta auka kusa da birnin New York

0
149

Wani rahoton Hukumar Kula da Duwatsu (USGS) ta Amurka ya bayyana cewar, da safiyar ranar Juma’ar, wata girgizar ƙasa ta auka wa yankin arewa maso gabashin birnin New York mai yawan jama’a, inda mazauna yankin suka ba da labarin jin motsin ƙasa, al’amarin da ba su saba ji ba.
Hukumar ta ba da rahoton samun girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 4.8 a ma’aunin richter da misalin ƙarfe 10 da mintuna 23 na safiyar ranar Juma’a kusa da yankunan Lebanon da New Jersey ko tazarar mil 45 yamma da birnin New York ko mil 50 arewa da Philadelphia.

Alƙaluman hukumar sun nuna cewar, me yiyuwa fiye da mutum milyan 42 sun ji motsawar ƙasar.

KU KUMA KARANTA:An ci Trump tarar dala miliyan 354.9 a New York

Hukumar ba da agajin gaggawa ta birnin New York ta wallafa a shafinta na sada zumunta mintuna 30 bayan samun girgizar ƙasar cewar, ba ta samu rahoton ɓarna ko jikkata a wani sashe na birnin ba.

A jawabinsa game da girgizar ƙasar, Magajin Garin Birnin New York, Eric Adams, wanda mai magana da yawunsa, Fabien Levy ya wakilta yace, “a yayin da muke dakon samun rahoton irin ɓarnar da girgizar ƙasar ta haddasa, har yanzu muna tattara bayanai akan tasirinta.

Al’umomin da suke zaune a yankunan Baltimore da Philadelphia da Connecticut da sauran sassan yankin arewa maso gabashin Amurka sun ba da rahoton jin motsin ƙasar.

An jiyo motsawar ƙasar tsawon daƙiƙoƙi daga nisan fiye da mil 200 kusa da kan iyakokin jihohin massachusetts da new hampshire.

Leave a Reply