Girgizar ƙasa a Haiti, majalisar ɗinkin duniya ta bayyana baƙin cikinta

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana baƙin cikinta yayin da wata mummunar girgizar ƙasa ta hallaka aƙalla mutane uku a kusa da birnin Jerémi na ƙasar Haiti da sanyin safiyar talata.

Hakan ya ƙara dagula al’amura da suka riga sun yi barazana ga rayuwa a ‘yan kwanakin nan sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa.

Girgizar ƙasar mai ƙarfin awo 5.5 ta auku a ma’aikatar Grand’Anse, biyo bayan mamakon ruwan sama da ya raba mutane sama da 13,000 da muhallansu.

KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano

Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya ce “Muna matuƙar baƙin ciki da asarar rayuka, da ɓarnata dukiya da kuma wahalhalun da al’ummar Haiti suka yi a sakamakon girgizar ƙasar.”

“Sakataren Janar, Antonio Guterres ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe tare da fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.”

Ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya a shirye take ta yi aiki tare da hukumomin Haiti da sauran abokan hulɗa, don taimakawa wajen rage wahalhalun da wannan sabon bala’i ya shafa.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ce hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta ce tuni ta fara bayar da agajin gaggawa ga waɗanda ruwan sama mai yawa ya shafa a ƙarshen mako, tare da samar da abinci mai zafi ga waɗanda suka rasa matsugunansu, tare da shirya kayan abinci da busassun abinci.

Dujarric ya ce Grand’ Anse na daga cikin wuraren da ruwan sama ya shafa, kafin girgizar ƙasar.

A cewar rahotannin labarai, girgizar ta ranar Talata ita ce ta biyu da ta auku a yankin cikin kwanaki biyu kacal, tare da yin girgizar ƙasa mai ƙarfin awo 4.4 a safiyar Lahadi.

A watan Agustan shekarar 2021, girgizar ƙasa mai ƙarfin awo 7.2 ta auku a yankin kudancin ƙasar, inda ɗaruruwan mutane suka mutu.

Ofishin kula da harkokin jin ƙai, (OCHA) yana aiki tare da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, WFP da Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, IOM, don tallafawa al’ummomin da ke kusa da babban birnin Port-au-Prince waɗanda ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa suka fi shafa.

Ya ƙara da cewa, WFP a shirye take ta raba wasu abinci mai zafi 350,000 da sauran taimakon abinci gaba ɗaya, ga waɗanda suka fi buƙata, in ji shi.

“Abokan aikinmu sun ce rashin tsaro da ake ci gaba da yi da lalacewar tituna suna kawo cikas ga duk wani aikin agaji.”

A cewar masu aikin jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa sun shafi bakwai daga cikin sassa 10 na ƙasar Haiti, kuma hukumomi sun ce aƙalla mutane 51 ne suka mutu, wasu 140 kuma suka jikkata, wasu 18 kuma sun bace.

A yankunan da abin ya shafa kusan gidaje 32,000 ne ambaliyar ta mamaye.


Comments

One response to “Girgizar ƙasa a Haiti, majalisar ɗinkin duniya ta bayyana baƙin cikinta”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa a Haiti, majalisar ɗinkin duniya ta bayyana baƙin cikinta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *