Gini ya rufto akan ɗalibai a GGSTC Potiskum, ɗaliba 1 ta rasu, 5 suna kwance a Asibiti
Daga Ibraheem El-Tafseer
Wani gini da ya rufto a kwalejin kimiyya fasaha ta ’yan mata ta GGSTC da ke ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe ya yi sanadin mutuwar ɗaliba ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
Abin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Alhamis, a lokacin da ɗaliban ke tsaka da karatu, abin da ya sa hukumomin makarantar suka yi gaggawar sanar da hukuma.
A rahotan da Neptune Prime ta tattara, ba zato ba tsammani ginin ya rufto, inda ya danne ɗaliban a ƙarƙashin baraguzan ginin. Jami’an agajin gaggawa sun kai ɗaukin gaggawa domin ceto waɗanda lamarin ya shafa.
An tabbatar da mutuwar ɗaliba ɗaya a wurin, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.
An garzaya da ɗaliban da suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na Potiskum, inda a yanzu haka suke samun kulawa.
KU KUMA KARANTA: Za mu yiwa filin jirgin saman Legas ginin zamani ; Ganduje
Kwamishinan Ilimi matakin farko da babbar Sakandare, Abba Idriss Adam, ya ziyarci wurin da rugujewar ginin ta auku tare da nuna alhininsa kan lamarin.
Kwamishina Idriss ya bayyana cewa, “Wannan wani lamari ne mai matuƙar takaici da ya jefa mu cikin baƙin ciki matuƙa. Zukatan mu suna miƙa gaisuwa ga iyalan yarinyar da ta rasa ranta a wannan lamari. Muna makoki tare da su kuma muna tarayya da su cikin raɗaɗin rashinta. Wannan rashi, babban rashi ne, ba kawai ga dangi ba amma ga dukkan al’umma.
Muna addu’ar Allah ya gafarta mata laifukan ta, ya kuma ba wa waɗanda suka samu raunuka lafiya. Ya kuma baiwa iyalanta haƙurin jure wannan rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.”
Ya kuma jaddada buƙatar yin cikakken bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin da kuma kiyaye aukuwar irin haka nan gaba.
“Mun ƙuduri aniyar gudanar da wani bincike don gano musabbabin wannan lamarin. Ba za mu bar wannan abu ba, sai mun gano inda matsalar ta samo asali. Mu tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin, kuma za mu ɗauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaron ɗaliban mu da ma’aikatanmu a dukkan cibiyoyin ilimi a faɗin jihar.”
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta bayar da dukkan tallafin da ya kamata ga iyalan waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar da cewa ɗaliban da suka jikkata sun samu kulawa mai inganci.
“Muna tuntuɓar juna da mahukuntan asibitin ƙwararru na Potiskum domin duba halin da ɗaliban da suka samu raunuka. Gwamnati za ta biya dukkan kuɗaɗen jinya tare da ba da duk wani ƙarin tallafin da ake buƙata don samun lafiyarsu cikin gaggawa.”
Neptune Prime ta lura cewa rushewar ginin ya haifar da damuwa game da ingancin tsarin gine-gine a cibiyoyin ilimi a faɗin jihar.
Mutane da yawa suna ƙira da a gaggauta bincika tare da gyara kayan makarantar don hana aukuwar irin wannan a nan gaba.