Gini ya faɗo ya kashe Fasto a Benuwe

0
236

Wani Fasto ya mutu bayan da wani ginin Cocin Dunamis da ke ofishin Ward North Bank a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwe ya ruguje da sanyin safiyar ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun bayyana cewa limamin cocin tare da wasu mutane na gudanar da addu’o’i a ginin cocin a lokacin da ya ruguje.  Wasu mutane ukun da ke harabar cocin sun tsere da ransu.

Gine-ginen gidaje da kayayyakin wutar lantarki da ke kewayen ginin sun ruguje.

Kawo yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.

Leave a Reply