Ghana na karɓar baƙuncin taron MƊD kan aikin sojojin wanzar da zaman lafiya

0
193

Ghana na karɓar baƙuncin taron kwana biyu kan aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka.

Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙira kan sojojin majalisar su bar ƙasashe da dama na nahiyar.

Ministoci da wakilai daga ƙasashe 85 suna gudanar da taron a Accra babban birnin Ghana daga 4 ga watan Disamba zuwa biyar ga watan na Disamba.

Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce ana yin wannan taron ne “domin samun goyon baya da kuma samun sadaukarwa domin karfafa ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD domin shawo kan ƙalubalen da ake fama da su a yanzu da na nan gaba.”

Mali da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Sudan su ne ƙasashen Afirka na baya-bayan nan da suke neman Majalisar Ɗinkin Duniya ta janye dakarunta inda suke cewa ba su da wani amfani tare da musu zargin take hakkin bil’adama.

KU KUMA KARANTA: Sojojin ƙasar Sudan sun bayyana aniyarsu ta komawa teburin shawara a Jeddah

A Mali, tuni dakarun na MƊD suka soma janyewa inda a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo kuwa, gwamnatin ƙasar da MDD sun amince tare da cimma matsaya kan janye dakarun.

A al’adance ana tura sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasashen da suke samun rashin zaman lafiya.

Babban aikinsu a kowace kasa suka je shi ne kwantar da tarzoma da samar da zaman lafiya.

Leave a Reply