No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Uwargidan Erdogan a ranar Talata ta bayyana mummunan yanayin da yara ƙanana ke fuskanta a Gaza a jawabinta na Ranar Kare Iyali, tare da yin tir da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa. Ta buƙaci haɗin kan duniya don karewa da tallafawa masu rauni.

Ta ce akwai akalla yara 17,000 da ke watangaririya ba tare da iyalansu ba a Gaza kuma ba su da inda za su je.

“A yau, abin takaici ne cewa a sassa daban-daban na duniya, yara suna rayuwa a cikin munanan yanayi, suna fafitikar rayuwa, balle a ce suna da damar rayuwa cikin jin dadi ta iyalai,” in ji Erdogan.

Ta jadada tsananin al’amarin, inda ta yi nuni da cewa, ana kyautata zaton yara 4,000 suke maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa ko kuma sun ɓata.

Erdogan ta ce yaran Falasdinawan da Isra’ila ta yi musu ta’asar da babu wani lamiri da zai goyi bayan hakan, an yi musu da tabon da ba zai warke ba.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Akalla Falasɗinawa 37,900 galibi mata da yara ne aka kashe yayin da 87,060 suka jikkata a Gaza tun lokacin da Tel Aviv ta kaddamar da farmaki a ranar 7 ga Oktoba, a cewar jami’an kiwon lafiya na yankin.

Fiye da watanni takwas da hare-haren Isra’ila, manyan yankunan Gaza sun zama kufai, a cikin yanayi na takunkuman hana shigar mata da abinci da ruwan sha da magunguna.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...