Gaza tana fuskantar tsananin ƙarancin abinci – WFP

0
166

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya wato World Food Programme (WFP) ya yi gargaɗi cewa akwai yiwuwar Gaza ya yi fama da matsanancin ƙarancin abinci, yana mai jaddada cewa abincin da ake kai wa bai isa ba wurin magance matasalar yunwa a yankin.

“Akwai matukar yiwuwar mutanen Gaza, musamman mata da ƙananan yara, za su fuskanci matukar ƙarancin abinci idan Shirin WFP bai ci gaba da samar da abinci ba,” in ji wata sanarwa da Shirin na WFP ya fitar.

KU KUMA KARANTA: An kashe Falasɗinawa 100 a hare-haren da aka kai musu cikin dare a Gaza

” WFP na matukar buƙatar abincin da zai bai wa fiye da mutum 120,000 a Gaza a matakin farko,” a cewar sanarwar.

Samer Abdeljaber, wakilin WFP kuma darakta a yankin Falasɗinu, ya ce tawagarsa ta ga yadda mutane suke cikin “yunwa da bala’i da rushewar muhallansu” kuma ba su samu agaji ko ɗaya ba cikin makonnin da suka gabata.

Leave a Reply