Gaza ba za ta kai labari ba idan aka sake rasa gadon kwantar da marasa lafiya a asibiti – WHO

0
108

Tsarin lafiya na Gaza ya kusa durƙushewa kuma yankin ba zai kai labari ba idan aka sake rasa motar ɗaukar marasa lafiya ko gadon asibiti, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargaɗi.

Kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya shaida wa taron manema labarai a Geneva cewa, “Al’amarin yana ƙara ta’azzara a kowace rana… fiye da zato.”

“Tsarin kiwon lafiya ya durkushe. Gaza ba za ta iya yin asarar wasu cibiyoyin kiwon lafiya ba, ko wata motar ɗaukar marasa lafiya guda ɗaya, ko wasu asibitoci… ko ma gadon asibiti guda ɗaya.”

KU KUMA KARANTA: Harin bam na Isra’ila ya kashe mutane da dama ya jikkata wasu a Birnin Gaza

Lindmeier ya ce yara da mutane suna “bara kuma suna kukan neman ruwa.”

“Muna kan wannan matakin, inda ba a samun kayayyakin yau da kullum da na yau da kullun,” in ji shi. “A yanzu ruwan da ake samu Gaza bai wuce lita ɗaya zuwa biyu ba a rana – wato ruwa rayuwa ne, ba kawai na sha ba. Wayewa ci gaba suna gab da wargajewa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here