Gayawa ‘yan Najeriya gaskiya gamaida tallafin man fetur – Bode George
Daga Ali Sanni
Jigo a jam’iyar adawa ta People’s Democratic Party wato PDP ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fito ya faɗawa ‘yan ƙasa gaskiyar lamari gamaida tallafin man fetur.
George wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ta PDP ne yace ‘yan ƙasa sun cancanci su san cewa gwamnatin Tinubu har yanzu tana biyan tallafin man fetur ta bayan fage.
Akwai jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin man fetur, tsohon gwamnan Bauchi dana Kaduna Isa Yuguda da Nasiru El- Rufai sun zargi gwamnatin yanzu da biyan tallafin man fetur fiye da da.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya bata bamu kuɗin tallafi ba – Gwamnan Oyo
Idan zaku tuna ministan kasafin kuɗi dana haɗe tattalin arziki Wale Edun ya sanar da cewa Najeriya tana kashe kimanin dalar Amurka miliyan 600 a kowane wata domin shigo da man fetur ƙasar.
Amma Bode George yace gwamnatin tarayya ta kasa bayyana wa ƴan kasar lamarin a fili.
Yace kanfanin mai na ƙasa NNPC mallakin gwamnatin tarayya ne kuma haka zalika mallakin ‘yan ƙasa ne. Don haka munaso musan maike gudana a chan.
George ya kara da cewa shi ba awannan bangaren yake ba amma yana iya sauraran A da B gamaida ma’aikatar ya yanke hukunci akan ko ɓangaren na bukatar gudummawar mu ko akasin hakan. Idan kuma da ɓarna mu bayyana ta.