Daga Ibraheem El-Tafseer
Najeriya ƙarƙashin mai horar da ƙungiyar Jose Peseiro za ta nemi kare maratabar ta da kuma neman ganin ta tsallaka mataki na gaba a wanan gangami,yayin da a ɗaya ɓangaren, Kamaru a cewar mai horar da ita, Rigobert Song za su kasance a kan bakar su na ganin sun doke Najeriya.
A tarihi, haɗuwar waɗannan ƙungiyoyi Najeriya da Kamaru a shekarun baya suka kasance gagara badau a fagen tamola, Najeriya da Kamaru sun haɗu sau 22. Najeriya ta samu nasara a wasanni 11 da ta buga da Kamaru. Yayin da Kamaru ta samu galaba a kan Najeriya sau huɗu ƙungiyoyin biyu sun yi canjaras sau bakwai.
A tarihin lashe kofin gasar Afirka na ƙwallon ƙafa baya ga Masar, da ta lashe Kofin sau 7, Kamaru ta ɗaga wannan kofi sau 5 sai Ghana sau 4.
A ɓangaren Najeriya, ƙungiyar Super Eagles ta lashe kofin sau uku, a shekarar 1980,1994 sai 2013.