Ganduje ya miƙa rahoton miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan Kano

1
217

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya gabatar da rahoton miƙa mulki na shekarar 2023 ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na zaɓaɓɓen gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar ranar Laraba a Kano.

A yayin wani ɗan taƙaitaccen taro da aka yi a ɗakin taro na gidan gwamnatin Kano, Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya jaddada ƙudirinsa na ganin an samu sauyi a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya buƙaci gwamnati mai zuwa da ta yi nazari sosai kan rahoton miƙa mulki tare da bayar da ra’ayi idan ya cancanta.

KU KUMA KARANTA: Za mu kawo ƙarshen shan miyagun ƙwayoyi a Kano – Ganduje

Gwamna Ganduje ya yabawa membobin kwamitin miƙa mulki na gwamnati bisa fitar da kundi uku na rahoton da ya ƙunshi dukkan sassan jihar.

A nasa jawabin, zaɓaɓɓen gwamnan wanda kuma shugaban kwamitin miƙa mulki na jam’iyyar NNPP, Dakta Baffa Bichi ya wakilta, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin nasa zai kai rahoto ga gwamna mai jiran gado, sannan ya koma tare da lura, idan akwai.

“A wannan lokacin, muna da sa’o’i 105 kacal don miƙa mulki a hukumance a jihar Kano, don haka mun himmatu wajen ganin mun kawo ƙarshen cikas domin amfanin Kano da al’ummarta,” in ji Bichi.

Ya ce za a bayyana cikakken bayani game da bikin rantsar da shi bayan an cimma wasu yarjejeniyoyin da aka ƙulla tsakanin gwamnatoci masu barin gado da masu jiran gado.

1 COMMENT

Leave a Reply