No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje, zai yi aikin miƙa ayyukan jihar a hukumance ga zaɓaɓɓen gwamnan, Abba Yusuf, yau Lahadi.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida mai barin gado Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa an gabatar da taron ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a gidan gwamnati dake Kano.

Ya ce tuni kwamitin miƙa mulki na gwamnatin jihar Kano ya sanar da ci gaban da kwamitin miƙa mulki na zaɓaɓɓen gwamnan ya yi.

Malam Garba ya yi nuni da cewa kwamitocin biyu sun gana ne a cikin satin da ya gabata inda aka gabatar da takardar miƙa wa kwamitin da aka zaɓa na gwamna, ya kuma ƙara da cewa sun kuma tsara shirin da ya dace kan bikin miƙa ragamar mulki.

KU KUMA KARANTA: Ganduje ya miƙa rahoton miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan Kano

Kwamishinan ya bayyana cewa, Ganduje zai tafi Abuja jim kaɗan bayan taron zai tafi Abuja a matsayinsa na shugaban tawagar Kano a bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ranar Litinin.

Ya ce ficewar gwamnan ya kuma zama dole don dokar wa’adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja don bikin kaddamar da shi.

Sanarwar ta yi ƙira ga jama’a da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...