Gamayyar Wasu Matasan Kaduna Sun Kudiri Aniyar Samar Da Kyakkyawar Zamantakewa Da Zaman Lafiya A Jihar

0
325

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GAMAYYAR wasu matasa daga sassa daban-daban da ke ciki da wajen Jihar Kaduna, wadanda ke karkashin wata Gidauniyar agaji ta Aid Foundation, sun Kudiri aniyar tabbatar da sun samar da Kyakkyawar zamantakewa da zaman lafiya a Jihar ta hanyar kawar da duk wasu banbance-banbancen addini ko na kabilanci a tsakanin al’ummar Jihar.

Matasan wanda a ranar lahadin da ta gabata wanda yake ranar zaman lafiya ta duniya, sun gudanar da wani taron menema labarai tare da Kaddamar da wani faifan waka a kan zaman lafiya a dakin wasannin motsa jiki na filin wasan Ahmadu Bello (ABS), dake Kaduna don shaida wa duniya irin matsayar da suka dauka bisa tabbatar da nasarar samun zaman lafiya a Jihar tare da tallafawar Gidauniyar Legacy.

Daya daga cikin mutanen da suke cikin tafiyar, Mohammed Mohammed ya bayyana cewa wannan wani babban al’amari ne wanda suka daukar wa kan su na ganin cewa zaman ya samu a tsakanin al’ummar Jihar tamkar yadda suke a shekarun baya ba tare nuna wani banbancin akida, kabilanci ko addini ba.

Ya kara da cewa, idan aka yi dubi da irin halin da ake ciki a shekarun baya, za a iya fahimtar cewa rayuwa na dadi kana da saukin gudanarwa kasantuwar duka mutane na zaune tare cikin kwanciyar hankali da amana da juna, amma daga baya wasu banbance-banbancen addini da kabilanci ya sanya duk abubuwa suka tabarbare.

Ya ce, “ada da muka taso, muna ganin kan mu tare yayin da muke gudanar da harkokin tare na zuwa makarantu, aiki, da kasuwanni, to amma daga baya duk al’amuran sun tabarbare ta yadda wasu yan uwanmu Musulmai suka kauracewa Unguwannin da suka taso ko aka haife su saboda rikicin kabilanci ko addini.

“Don haka a yanzu muka ga ya dace ace an warware wannan matsalar ta rashin fahimta da lalacewar zamantakewar wanda ya haifar da duk wata damuwar da muke ciki na rashin zaman lafiya a tsakanin mu, shi yasa a yanzu muka ga ya kamata mu tabbatar da an dawo da wannan zaman lafiya tare da taimakon ita wannan Gidauniya ta Aid Foundation wacce ta ke jagorantarmu.

Hakazalika, wani matashi daga Sabon Tasha, ya bayyana cewa wannan aikin neman samar da Kyakkyawar zamantakewa da zaman lafiya da suka dauka, sun kudiri aniyar yin hakan ne sanin cewa babu wata mafita ga al’ummar Jihar Kaduna wacce ta ke fiye da samar da zaman lafiya domin ta haka ne kadai za a iya samun duk wata ci gaban da ake bukata a Jihar.

Acewarsa, akalla shekaru talatin da suka gabata, sun saba gudanar da rayuwa cikin lumana tare sauran yan Uwansu wanda suke Musulmai duk da cewar su Kiristoci ne, amma hakan bai kasance wani nakasu a gare ba domin suna gudanar y rayuwa cikin jin dadi da walwala kana tafiya yadda ya dace ba tare wata matsala ba.

Ya ce “amma tun daga bayan lokacin da aka yi fadan Shari’a, duk Musulman da ke zaune a Unguwannin da Kiristoci suka fi karfi ko yawa, duk sai suka watse, haka suma Kiristocin da ke zaune a cikin al’ummar Musulmi sai suka canza wuri suka koma cikin sauran yan Uwansu Kiristoci saboda zaman lafiyar ya gagara kuma ba dadi a kan jituwa.

“To a yanzu, mun dauko wannan aikin ne saboda nuna wa duniya cewa zamu iya zama daya ta hanyar girmama juna tare da kauracewa duk wani rudani da zai iya kawo hatsaniya ko rashin jituwa a cikin al’ummarmu wadanda ada an san mu tare kuma tare muke duk wasu huldodin mu na yau da kullum, don haka ba zamu gaji ba har sai mun tabbatar da nasarar samun wannan zaman lafiya a Jihar.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa, babban Daraktan Gidauniyar, Emmanuel Bonet, ya bayyana Jin dadinsa bisa irin yadda Matasan suke kokarin ganin cewa an magance wannan matsalar ta rashin fahimta da aminci a tsakanin juna, musamman a tsakanin al’ummar Kirista da Musulmai, wanda hakan ne ya sanya matasan daga Unguwanni daban-daban suka hada kan su domin ganin sun cimma wannan matsaya na cikar burin su a kan samar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa Gidauniyar wacce ta ke mai zaman kanta a Jihar Kaduna na duk iya bakin kokarinta na ganin cewa ta samar wa da matasan duk taimakon da su ke bukata, musamman ta hanyar tallafawa mu su ta fannin yin karatu da samun ayyukan da zasu dogaro da kansu domin ta hakan ne za a iya samun nasarar da suke bukata.

Bonet ya ci gaba da cewa a yanzu suna Kokarin ganin yadda zasu hada kai da Gwamnatin Jihar wanda a halin yanzu sun fara samun goyon bayan ma’aikatar tsaro da harkoki na musamman don ganin cewa an aiwatar da al’amuran yadda ya kamata ta hanyar wayar da kan al’umma kan Muhimmancin samar da Kyakkyawar zamantakewa da zaman lafiyar a tsakanin al’ummar Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here