Gadar sama ta ruguje a kan titin Inugu zuwa Fatakwal

0
242

Ɗaya daga cikin gadar sama da ke kan titin Inugu zuwa Fatakwal mai hawa biyu a Inugu ta ruguje ba tare da wani asarar rai ba.

Gadar wadda ta ruguje a safiyar ranar Litinin, tana da tazarar kilomita ɗaya ne a kan babban titin da ke tsakanin titin Naira triangle da kuma sabuwar ma’adanin sana’a na birnin Inugu.

NAN ta lura cewa lamarin ya tilastawa masu ababen hawa da ke bin titin mota karkata zuwa wasu hanyoyin da ke cikin babban birnin domin ci gaba da tafiya.

Jami’an ‘yan sanda, jami’an ma’aikatun ayyuka na tarayya da na jihar Inugu, da hukumar kula da tituna ta tarayya, (FEMA), da hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya, (FRSC), an gansu a yankin domin ganin halin da ake ciki da kuma taimakawa masu amfani da hanyar.

KU KUMA KARANTA: Mutane 17 sun mutu sakamakon rugujewar gadar jirgin ƙasa ta Indiya

Wani ganau wanda ya bayyana sunansa da John Nwokobia, ya ce ba a samu asarar rai ba saboda har yanzu masu sana’ar hannu da ɓarayin tituna ba su fito daga gidajensu domin gudanar da harkokinsu na ranar a lokacin da lamarin ya faru ba.

Shaidan ya lura da cewa masu ababen hawa a kan gadar na iya fuskantar matsala mai tsanani sakamakon rugujewar gadar a cikin kwanaki masu zuwa.

Har yanzu dai ‘yan sanda, gwamnatin tarayya ko na jihohi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba har ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton.

Leave a Reply