No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gada ta yanke tsakanin Azare zuwa Maiduguri

Daga Idris Umar, Zariya

Wata Gada da ke garin Buskuri kusa da Azare, ta yanke sakamakon yadda wani katafaren kogi da ya biyo ta samanta.

Mutanen yankin sunce Ruwan da yake biyowa ta Gadar yafi ƙarfin Gadar.

Kogin ya taso ne tun daga yankin Giyaɗe ya biyo ta garin Zadawa shi ne har garin Buskuri dake kan hanyar zuwa Maiduguri ya haura ya shiga jeji.

Haka zalika wasu Rahotannin sunce Gadar Dab da shigowa garin Zabi ita ma ta cika maƙil da ruwa wanda hakan ta kai da ruwan ya tunkari garin Faguji da ke yankin Giyaɗe ance wata mota ƙirar Homa ma ta faɗa a garin.

Haka zalika Gadar garin Zadawa ma ta yi wannan cikar.

KU KUMA KARANTA;Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

Yanzu haka dai dukkan waɗannan garuruwan da ma wasu na fuskantar barazanar ambaliyar Kogunan da ke kusa da garuruwan nasu.

Ruwan sama da Allah ya kawo mai ƙarfin gaske shi ne silar wannan ambaliyar.

Bincike ya nuna cewa kusan Awa sha 12 aka ɗauka ana zub da ruwan saman a ranar Laraba da
A ranar Alhamis kuma ruwan saman ya ci gaba da sauƙa har wayewar garin juma’a.

A ranar Alhamis Gwamnan jihar Bauchi muhammad Bala Ƙaura ya kawo ziyara a garin Azare don ganin abubuwan da ya faru a lokacin zanga-zangar ne man sauƙin rayuwa. Don haka ne ma ake ganin gwamnan zai ga halin da waɗannan koguna suke ciki kuma ana tunanin zai bayar da taimakon gaggawa da zai taimaki garuruwan da ke kusa da kogunan da lamarin ke faruwa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...