Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa – NCS

0
84
Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa - NCS

Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa – NCS

Hukumar da ke Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCS), ta ce fursunoni 281 ne, suka tsere sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafe wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Kakakin hukumar, Umar Abubakar, ya ce: “Wannan lamari mara daɗi ya haifar da ɓarna, inda ya rushe katangarar gidajen gyaran hali da suka haɗa da matsakaicin cibiyar tsaron hukumar ta Maiduguri (MSCC).”

Ya bayyana cewa: “Bayan kwashe fursunonin da jami’an hukumar tare da tallafi daga jami’an tsaro zuwa wani waje mai tsaro, sai aka gano fursunoni 281 sun ɓace.”

KU KUMA KARANTA: Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri na fuskantar matsalar lafiya – NRC

Ya ƙara da cewa hukumar tana da bayanan fursunonin da suka tsere

Ya ce: “Hukumar tana aiki tare da sauran jami’an tsaro saboda an fara aikin a ɓoye domin ƙara kama su.

“A yanzu haka, an sake kama fursunoni bakwai tare da mayar da su gidan yari, yayin da ake ƙoƙarin gano sauran don a dawo da su.

“Yayin da ake wannan ƙoƙarin, akwai tabbacin cewa lamarin ba zai kawo cikas ba ko kuma ya shafi lafiyar jama’a ba.”

Leave a Reply