Fursunoni 118 sun tsere daga gidan yarin Suleja

0
142

Daga Idris Umar, Zariya

Fursunoni kimanin 118 sun tsere bayan ruwan sama ya rusa katangar gidan yarin Suleja da ke Jihar Neja a daren ranar Laraba.

Jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a lunguna da sakunan garin Suleja da kewaye a yunkurinsu na kamo wadanda suka tsere.

An ce fursunonin sun tsere daga gidan yarin ne bayan wata iska mai karfin gaske da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya rushe sashin katangar gidan da suke tsare a ciki.

Wani mazaunin garin, ya shaida wa kafar yada labarai cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke gadi, suka tsere ta hanyoyi daban-daban, inda wasu daga cikinsu suka yi ta jifan jama’ar garin da suka yi yunkurin tare su.

Ganau din ya ce, “Jifan da fursunonin ke yi ya lalata wasu motocin da ke ajiye a bakin hanya a cikin garin Suleja.”

KU KUMA KARANTA: Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin Comoros

Hukumomin tsaro sun ce an kama uku daga cikin fursunonin a cikin daren Laraba a unguwannin da ke kewaye da gidan yarin.

An kuma kama wasu da dama da safiyar Alhamis a Unguwannin Rafin Sanyi da Kwankwaso da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla.

wakilan kafafen yada labarai da dama sunyi kokarin yin magana da kwamandan ’yan sandan yankin Suleja, ACP Muhammad Sani Musa, amma basuyi nasara ba, har zuwa haɗa wannan rahoton.

Za muci gaba da bibiyar yadda lamarin zai gudana don kawowa masu karatummu

Leave a Reply