FRSC ta buƙaci a kawo rahoton tuƙin ganganci a kan tituna

0
32
FRSC ta buƙaci a kawo rahoton tuƙin ganganci a kan tituna

FRSC ta buƙaci a kawo rahoton tuƙin ganganci a kan tituna

A ranar Juma’a, hukumar kare aukuwar hatsurra ta Najeriya (FRSC) ta buƙaci matafiya su kai rahoton tuƙin ganganci akan tituna domin rage yawaitar afkuwar hatsura a watannin karshen shekarar bana.

FRSC ta yi wannan kira ne bayan da ta kammala gangaminta na wayar da kan al’umma a kan watannin karshen shekara.

Taken gangamin na bana shine “yi magana a kan tukin ganganci: hatsura sun fi hallaka fasinjoji fiye da direbobi”.

KU KUMA KARANTA:Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

A ranar 6 ga watan Nuwambar da muke ciki, reshen jihar Filato na hukumar ta FRSC ya kaddamar da nasa gangamin wayar da kan al’ummar a birnin Jos.

A jawabinsa yayin bikin kaddamar da gangamin, Kwamandan FRSC na jihar, Maxwell Plateau, ya jaddada bukatar samun sauyin dabi’a a tsakanin direbobi.

Ya jaddada cewa fasinjoji na da hakkin a tukasu cikin aminci tare da karfafa musu gwiwar jan kunnen direbobin da suka karya dokokin tuki.

Leave a Reply